Mu Zagaya Duniya

Annobar coronavirus ta kashe sama da mutane 438,250 a fadin duniya

Sauti 20:11
Daya daga cikin jami'an kiwon lafiya dake yaki da cutar Coronavirus
Daya daga cikin jami'an kiwon lafiya dake yaki da cutar Coronavirus Getty Images via AFP

Annobar coronavirus ta kashe mutane 438,250 a fadin duniya, bayan ta kama mutane miliyan 8, da dubu 90,290, yayin da miliyan 3 da dubu 698,500 suka warke.A cikin sa’oi 24 da suka gabata, cutar ta kashe mutane 3,851, yayin da aka samu sabbin kamu 114,921, kuma akasarin wadanda suka mutu sun fito ne daga Amurka mai mutane 671, sai Brazil mai mutane 627 sai kuma Mexico mai mutane 439.A nahiyar Turai kawai cutar ta kashe mutane 188,834, sai Amurka da Canada da suka yi asarar mutane 124,826, sai Gabas ta Tsakiya mai mutane 12,234 sannan Afirka mai mutane 6,792.Garba Aliyu a cikin shirin Mu Zagaya Duniya ya duba mana halin da ake ciki a sassan Duniya tareda dubo wasu labaren can daban.