Gwamnonin Najeriya sun dauki hayar mafarauta don maganin 'yan bindiga
Gannin yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a yankin arewacin Najeriya, yanzu haka Gwamnonin da suka fito daga Yankin sun yanke shawarar daukar mafarauta da kungiyoyin sa kai domin taimakawa wajen aikin samar da tsaro a Jihohin su.Wannan ya biyo bayan cigaba da kashe kashen da ake samu a Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma wasu yankunan arewacin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bayan wani taro da suka gudanar ta kafar bidiyo domin nazarin tabarbarewar tsaron a karkashin shugaban su kuma Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong, Gwamnonin sun bayyana matukar damuwar su kan lamarin wanda ke cigaba da lakume rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyi.
Taron ya amince a kafa wani kwamitin tsaro na musamman a karkashin Gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello wanda zai taimaka wajen hada kai da bangarorin jami’an tsaro wajen samun nasarar kawo karshen matsalar.
Sanarwar bayan taron tace Gwamnonin sun kuma amince su kafa wani kwamitin tintiba a karkashin Gwamnan Plateau Simon Lalong wanda zai gana da Sarakunan Gargajiya da shugabannin addinai da shugabannin jama’a domin basu damar taka rawa wajen shawo kan matsalar.
Taron ya amince da baiwa kungiyoyin Yan sa kai da mafarauta da Yan banga damar taka rawa wajen tattara bayanan asiri domin taimakawa jami’an tsaro.
Gwamnonin da suka jajantawa yan uwa da iyalan wadanda aka kashe ko aka jikkata a hare haren Yan bindigar sun bukaci jama’a suyi hakuri don suna hada kai da gwamnatin tarayya wajen ganin an gaggauta kawo karshen lamarin da kuma tallafawa wadanda hare haren ya ritsa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu