Najeriya-'Yan bindiga

Harin 'yan bindiga ya sake kashe wasu mutum 8 a Katsina

Hare-haren 'yan bindigar na ci gaba da tsananta a jihar Katsina duk da ikirarin gwamnati na daukar matakan dakilesu.
Hare-haren 'yan bindigar na ci gaba da tsananta a jihar Katsina duk da ikirarin gwamnati na daukar matakan dakilesu. Daily Trsut

Rahotanni daga Jihar Katsina da ke Najeriya sun ce 'yan bindiga sun sake kai hari daren jiya a garin Kasai da ke karamar Hukumar Batsari inda suka kashe mutane 8.

Talla

Wani mazaunin garin ya shaidawa sashen hausa na RFI cewa an kai harin ne da misalin karfe 11 da rabi, inda 'yan bindigan suka yi ta harbe harbe na sa’oi sama da 2 kafin daga bisani su ka fice daga garin.

Shaidar gani da idon ya shaida mana cewar lokacin da 'yan bindigar ke harbe-harben jirgin saman sojin Najeriya ya je inda yayi ta shawagi amma kuma bai yi harbi ba.

Majiyar ta mu ta ce bayan ficewar 'yan bindigar daga garin sun samu gawar mutum  guda, amma kuma bayan wayewar gari suka samu karin gawarwakin wasu mutane 7 a cikin ruwa dauke da harbin bindiga a jikinsu.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da 'yan bindiga ke cigaba da kai hare hare ba tare da kaukautawa ba a Arewacin Najeriyar mai fama da karancin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.