Najeriya

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta nemi dakatar da zanga-zanga

Wasu daga cikin shugabanin arewa a lokacin zabe a garin Daura dake Najeriya.
Wasu daga cikin shugabanin arewa a lokacin zabe a garin Daura dake Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta bukaci kungiyoyin matasan da ke yankin da su dakatar da zanga zangar lumana da suka shirya domin nuna bacin ran su kan tabarbarewar tsaro a yankin, maimakon haka kungiyar ta nemi lalubo wasu hanyoyin da za su matsawa gwamnatin jiha da ta tarayya lamba wajen daukar matakan kawo karshen wadannan kashe kashe.

Talla

Kungiyar ta kuma shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin Jihohi cewar kada su dauke su a matsayin barazana a gare su, sai dai a matsayin wadanda suke taimaka musu wajen janyo hankalin su kan halin da ake ciki a Yankin arewa domin daukar matakan da suka dace.

Daraktan yada labaran kungiyar Dr Hakeem Baba Ahmed yace kungiyar ta su ta bukaci duk wasu kungiyoyin jama’a dake arewacin Najeriya da su tashi tsaye wajen janyo hankalin zababbun wakilan su da su sauke nauyin dake kan su wajen tabbatar da shugabanci na gari da kare rayukan jama’a.

Dr Ahmed yace kafin gudanar da zaben shugaban kasa sun shaidawa shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin Jam’iyyar sa ta APC muhimmancin inganta matakan tsaro, saboda haka ya dace su sauke wannan nauyi da ya rataya a kan su.

Dangane da zanga zangar lumana da matasa keyi kuwa, tsohon Babban Sakataren Gwamnatin tarayyar yace sun samu labarin cewar wasu na shirin tada hankali lokacin gudanar da zanga zangar a wasu garuruwa, saboda haka sun bukaci kungiyoyin dake shirya zanga zangar da su dakatar da haka, domin bukatar su itace ganin an janyo hankali amma ba tada hankali ba.

Kungiyar ta kuma ce ta gamsu da yadda zanga zangar lumanar da aka yi a Jihohin Katsina da Niger suka gudana, da kuma abinda ya biyo baya wajen tura manyan jami’an tsaron kasa zuwa yankunan da ake samun matsala da kuma yadda shugaban kasa ya shaidawa hafsoshin sojin cewar bai gamsu da rawar da suke takawa ba.

Dr Hakeem yace wannan shaida ce cewar gwamnatin na sauraron korafin dake fitowa daga cikin al’umma da kuma rawar da kungiyoyin matasan ke takawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.