Libya-Masar

Libya ta yi watsi da shirin sasanta rikicin kasar bisa jagorancin Masar

Wasu hare-haren bangarori masu rikici da juna a Libya.
Wasu hare-haren bangarori masu rikici da juna a Libya. Getty Images

Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta yi watsi da shirin sasanta rikicin kasar da kungiyar kasashen larabawa karkashin jagorancin Masar ta gabatar.

Talla

Karkashin shirin dai a mako mai zuwa ne aka tsara ganawar ministocin wajen kasashen na larabawa don tattaunawa da nufin sasanta tsakanin bangarori biyu masu rikici da juna a Libyan, sai dai ma’aikatar harkokin wajen Libyan ta ce ko kadan ganawar ba ita ce mafita ba.

Cikin jawabin da ministan harkokin wajen Libyan Mohamad Taher Siala ya gabatar gaban kusoshin gwamnatin kasar jiya Juma’a, ya ce ganawar ba komai za ta haifar ba face karin rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnatocin kasashen na Larabawa.

Ganawar karkashin jagorancin masar da aka tsara za ta gudana ta bidiyon Intanet saboda coronavirus, Siala ko kadan ba ta shafe su ba, musamman kasancewar Masar babbar mai goya baya ga Khalifa Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI