Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kwantar da hankula a Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kwantar da hankula a Mali bayan zanga-zangar jiya Juma’a da dubban al’ummar kasar suka gudanar kan neman shugaba Boubacar Keita ya yi murabus.

Dandazo masu zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Bamako na Mali.
Dandazo masu zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Bamako na Mali. AFP/Michèle Cattani
Talla

Babban magatakardar Majalisar Antonio Gutteres ta bakin mataimakinsa Farhan Haq ya nemi bangarorin adawa su daina tunzura magoya bayansu don gudun sake rikicewar kasar da ke fama da hare-haren ta’addanci tun 2012.

Zanga-zangar ta jiya wadda ita ce irinta ta biyu a watan nan bangaren adawa ya sha alwashin bijirewa umarnin gwamnati kan fararen hula matukar bukata bata biya ba game da neman saukar shugaban daga mulki.

Boubacar Keita wanda aka sake zabensa a 2018 tun bayan sake hawansa mulki al’amuran tsaro ke ci gaba da tabarbarewa baya ga rikicin siyasar kasar karuwar rashin aikin yi da kuma yawaitar yajin aikin ma’aikata galibi malaman makaranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI