Masar ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakaninta da Habasha

Shugaba Abdel Fattah al-Sissi, na Masar.
Shugaba Abdel Fattah al-Sissi, na Masar. AFP/Egyptian Presidency/Str

Kasar Masar ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya baki wajen sasanta rikicin dake tsakanin kasar da Sudan da Habasha dangane da gina madatsar ruwan da zai hana ta samun ruwan da take samu daga kogin Nilu.

Talla

Kiran na zuwa ne sakamakon samun Karin tankiya a tsakanin kasashen dake makotaka da juna bayan duk wani yunkurin sasantawa da akayi ciki harda wanda Amurka ta shiga tsakani ya ci tura.

Tuni Habasha ta sanar da cewar daga watan gobe zata fara karkata akalar ruwan zuwa cikin madatsar da zai taimaka mata samun wutar lantarki, yayin da Masar ke cewa hakan ba zai yiwu ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da gabatar da bukatar kasar a kwamitin sulhu domin shiga tsakani da kuma kaucewa tashin hankali.

Ita dai Habasha ta bayyana aikin a matsayin mai muhimmanci ga rayuwar ta da zai taimaka mata wajen samun cigaba, yayin da Masar tace kasha 97 na ruwan da ta dogara da shi ya fito ne daga kogin Nilu, saboda haka aikin zai hana ta samun kasha 97 na ruwan da ta dogara da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI