Afrika

Masu zanga-zanga na neman Keita ya sauka daga shugabancin Mali

Dubban mutane ne a jiya juma’a suka halarci jerin gwanno a tsakkiyar birnin Bamako na kasar Mali inda suka bukaci shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta ya yi murabus,

Masu zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali
Masu zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali AFP/Michèle Cattani
Talla

Zanga-zangar na zuwa ne a karo na biyu karkashin kiran da gamin gambizar kungiyoyin siyasa da na farar hula da addini suka yi wa alúmmar kasar ne da su fito domin tilastawa shugaban Keita murabus kan abinda suka kira tabarbarewa komai a kasar dake fama da tashe tashen hankullan kungiyoyin jihadi .

Kungiyar kasashen ECOWAS ta aike da wakilan ta da suka gabatar da shawarwari don samun mafita a wannan rikici na kasar Mali.

Daga cikin shawarwarin da suka gabatar da su ,akwai zancen sake gudanar da zaben wakilan majalisa a wasu yankuna da ake zaton zaben bai gudana cikin gaskiya ba.

Sai dai ya zuwa yanzu masu bore su bayyana cewa za su ci gaba da bore har sai su kai ga cimma burin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI