Amurka

Masu zanga-zanga sun kawar da mutun-Mutumin Albert Pike

Dubban mutane ne suka taru a jiya juma’a a biranen New York da Los Angeles na kasar Amruka domin tunawa da cika shekaru 155e "Juneteenth" ranar da aka yantar da bayin karshe a 1865 a Texas. Wasu daruruwan mutane kuma sun yi jerin gwano a Washington a karkashin kiran da kungiyoyin kwallon kwandon yankin suka yi domin nuna bacin ransu da hallayar kabilanci da kuma tursasawar da yan sanda ke yiwa bakar fata.

MUTUM -MUTUMIN Albert Pike da masu zanga-zanga suka tono
MUTUM -MUTUMIN Albert Pike da masu zanga-zanga suka tono RFI
Talla

A yau wasu daga cikin masu zanga –zanga sun kawar da wani Mutun-mutumin wani janar da aka dasa a Washington. .Daya daga cikin tashoshin kasar da aka sani da ABC7 ce ta yada bidiyo dake nuna ta yada wasu mutane ke kawar da Mutun m-mutumin Albert Pike tareda ikirarin kare mutucin bakar fata, lamarin da Shugaban Amurika Donald Trump a wani sako da ya aike ta twitter cewa abin kumya ne,ya kuma bukaci yan sanda sun kama mutanen da suka aikata wannan aika-aika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI