Kotu ta zartas da hukuncin daurin shekaru 20 ga Vital Kamerhe
Kotu a jamhuriyyar demokradiyyar congo ta zartas da hukuncin daurin shekaru 20 ga Vital Kamerhe shugaban ma’aikatan fadar shugaba Felix Tshisekedi bayan samun da laifin karkatar da kudaden gwamnati da yawansu ya kai dala miliyan 48 da dubu dari 8 tareda hada baki da wani dan kasar Lebanon.
Wallafawa ranar:
Shari’ar wadda ta gudana a kotun Kinshasa, hukuncin ya bukaci sanya Kamerhe ayyukan wahala yayin zaman na gidan yarin inda kuma aka haramta masa shiga harkokin siyasa na shekaru 10 bayan kammala wa’adinsa na Yari.
Sai dai Lauyan Kamerhe mai shekaru 61, jean Marie ya ce za su daukaka kara don kalubalantar hukuncin kotun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu