Najeriya-Lafiya

Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka tsunduma

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta sanar da janye yajin aikin da mambobinta suka tsunduma daga gobe litinin 22 ga watan Yuni biyo bayan ganawar uwar kungiyar da gwamnati kan bukatun da suka tilasta musu tafiya yajin aikin gargadin.

Wasu Likitocin Najeriya.
Wasu Likitocin Najeriya. RFI Hausa
Talla

Cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta raba mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Dr Aliyu Sokomba, ta ce sun dauki matakin janye yajin aikin ne don baiwa gwamnatocin jihohi da tarayyar damar cika alkawuran da suka dauka.

Acewar sanarwar tun farko shugaban majalisar wakilan kasar Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnati Boss Mustapha da kuma shugaban kungiyar gwamnonin kasar Kayode Fayemi ne suka shiga tsakanin gabanin amincewa da matakin janye yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI