Turai

Mutane uku sun mutu a wani harin wuka a Birtaniya

Wurin shakatawa na Reading  dake Britaniya
Wurin shakatawa na Reading dake Britaniya Adrian DENNIS / AFP

A Birtaniya, da misalin karfe bakwai na yammacin jiya asabar wani mutum dauke da wuka ya kashe mutane uku tareda raunata wasu uku a wani wurin shakatawa dake Reading a yammacin birnin Landan.

Talla

Yan sanda sun bayyana cewa wannan hari ba shida halaka da ta’addanci, duk da haka bincike na tafiya a kai inda aka bayyana cewa yan sanda zasu samu taimakon hukumar yakin da ta’addanci a kasar a cewar Shugaban yan Sanda Ian Hunter a Birtaniya.

Ministan cikin gidan Birtaniya Priti Patel ta bayyana takaicin ta tareda nuna damuwa a kai,yayinda Firaministan kasar Borris Johnson ya aike da sakon jimami ga iyalan mutanen da suka rasa na su da kuma aka jikkata .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI