Afrika

Tsohon Shugaban Cote D'Ivoire na neman kujerar shugabancin kasar

Henri Konan Bédié,tsoho Shugaban kasar Cote D'Ivoire kma dan takara a zaben shekara ta 2020
Henri Konan Bédié,tsoho Shugaban kasar Cote D'Ivoire kma dan takara a zaben shekara ta 2020 SIA KAMBOU / AFP

A Cote D’ivoire tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie mai shekaru 85 cikin daren jiya asabar ya sanar da aniyar sa ta shiga jerryn masu neman kujerar shugabancin kasar sa Cote D’Ivoire a jam’iyyar sa ta PDCI.

Talla

Tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie a yayi da yake sanar da takarar sa ya na mai cewa ya sadaukar da kan sa,tareda kira ga magoya bayan jam’iyyar PDCI na ganin sun bayar da nasu goyan baya a wannan tafiya don samun nasara a zaben Shugabancin kasar na ranar 31 ga watan oktoba na wannan shekara.

A shekara ta 1999 ne sojoji suka kiffar da gwamnatin Henri Konan Bedie, wanda ya kuma kulla yarjejeniya da Shugaban kasa mai ci Alassane Dramane Ouattara kafin sun raba gari.

Dan takara na uku a zaben kasar da suka sanar da takarar su bayan Guillaume Soro tsohon Shugaban majalisa dake gudu hijira a Faransa,kana bangaren gwamnati said an takara Amadou Gon Coulibaly firaminista mai ci yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.