AU ta bukaci Mali ta hada kai da 'yan adawa don magance rikicin siyasarta
Wallafawa ranar:
Shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afirka AU Moussa Faki Mahamat ya bukaci shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da ya yi aiki tare da 'yan adawa domin kawo karshen rikicin siyasar da ya mamaye kasar.
Mahamat wanda ya yaba da yadda zanga zangar 'yan adawar Mali ke gudana cikin kwanciyar hankali, ya bukaci shugaba Keita da ya saurari koke koken su domin kaucewa tashin hankali.
'Yan adawar Mali na bukatar shugaban kasar da ya sauka daga mukamin sa saboda abinda suka kira gazawa wajen kare yan kasar da ake cigaba da hallakawa da kuma kasa dakile rikicin kabilanci.
Shugaba Keita ya sha alwashin kafa gwamnatin hadin kai tare da 'yan adawar, amma sun ki amincewa da tayin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu