Ghana ta nemi gafarar Najeriya kan rusa mata ginin Diflomasiyya

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. REUTERS/Hannah McKay/File Photo

Kasar Ghana ta nemi gafarar Najeriya kan yadda aka rusa ofishin Jakadancin ta a kasar, yayin da ta kaddamar da bincike domin gano dailin rusa ginin.

Talla

Mataimakin ministan harkokin wajen Ghana Charles Owiredu ya bayyana takaici kan rusa ginin, wanda yace hurumin gwamnatin Ghana ce ta kare shi kamar yadda dokar diflomasiya ta tanada.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya bayyana matakin a matsayin ta’addanci.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro dauke da makamai suka raka motar da ta rusa sabin ginin a karshen mako, matakin da ya haifar da suka mai karfi daga ciki da wajen Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI