Bakonmu a Yau

Kwamishinan yada labaran Plateau Dan Manjang kan yadda NNPC ta gano Fetur a jihar

Sauti 03:09
Ginin katafaren kamfanin man Najeriya NNPC
Ginin katafaren kamfanin man Najeriya NNPC REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Katafaren Kamfanin man Najeriya na NNPC ya sanar da samun arzikin man fetur a kananan hukumomin Wase da Kanam dake Jihar Plateau, matakin da zai sanya Jihar cikin jerin Jihohin dake da arzikin man.

Talla

Tuni wannan labari ya farantawa al’ummar jIhar rai, bayan binciken da Kamfanin tare da Jami’ar Jos suka yi, kamar yadda shugaban kamfanin Mele Kyari ya shaida a ziyarar da ya kai Jihar.

Dangane da wannan cigaba, mun tattauna da kwamishinan yada labaran Jihar, Dan Manjang, kuma ga bayanin da yayi mana akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.