ECOWAS ta mara baya ga takarar Ngozi Okonjo-Iweala kan shugabancin WTO
Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma ta bayyana goyan bayan ta ga takarar tsohuwar ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala na takarar kujerar shugabancin kungiyar kasuwanci ta Duniya, wato WTO.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar da cewar shugabannin ECOWAS sun amince da takarar Madame Ngozi saboda kwarewar ta da kuma jagorancin da tayi a irin wadannan hukumomi a baya.
Kungiyar kasashen Afirka ta bayyana shirin gabatar da dan takara guda daga nahiyar domin ganin an samu nasarar wanda zai jagoranci kungiyar daga Afirka.
Cikin masu neman kujerar harda tsohon Jakadan Masar, Hamid Mamdou, yayin da Afirka da bata taba rike shugabancin kungiyar ke bayyana fata a wannan karo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu