Bakonmu a Yau

Tattunawa da Sanata Mohammed Ali Ndume kan ziyararsu ga Gwamnan Jihar Borno game da matsalar tsaro

Wallafawa ranar:

Tawagar ‘yan majalisar Dattawan Najeriya karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye Sanata Yahaya Abdullahi sun ziyarci Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum don jajantawa alummar Jihar harin baya-bayan nan da mayakan Boko Haram suka kaddamar da kuma tattaunawa kan matsalolin tsaron yankin na Arewa maso gabshin kasar ke fuskanta.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum tare da wasu Mambobin Majalisar Dattijan Najeriya a ziyarar ad suka kai masa.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum tare da wasu Mambobin Majalisar Dattijan Najeriya a ziyarar ad suka kai masa. RFI Hausa
Talla

Tawagar ‘yan majalisar dattawan da suka hada da Sanata Orji Uzor Kalu da Yahaya Alhaji Yawu da Kashim Shettima da Mohammed Ali Ndume sai kuma Abubakar Kyari, sunyi alkawarin bincikar abin da ya hana ruwa gudu a yaki da rikicin Boko Haram wanda ke ci gaba da lakume rayukan Jama'a.

Kan haka ne muka tattauna da Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke cikin tawagar kuma shugaban kwamitin majalisar da ke kula da ayyukan soji, wanda ya yi mana karin haske kan dalilai dama muradan da suke fatan cimmawa a jihar ta Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI