Nijar

An gano hujjojin da ke tabbatar da badakala a cinikin makaman Nijar

Wasu Sojin Nijar da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel.
Wasu Sojin Nijar da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel. Ludovic MARIN / POOL / AFP

Mai gabatar da kara a Jamhuriyar Nijar Mamma Sayabou Issa ya tababtar da samun shaidun da ke bayyana aikata laifuffuka a badakalar sayen makaman sojin kasar wanda ya kai euro miliyan 50.

Talla

Jami’in ya ce shaidun sun hada da kara kudaden makaman da kuma rashin aiwatar da wasu kwangilolin, abinda ya haifar da mahawara mai zafi a cikin kasar, musamman bayan kasha sojojin da ke yaki da yan ta’adda.

Rahotan binciken ya tabbatar da aikata laifi wajen aiwatar da kwangilar da kuma zargin azurta kai da aikata laifi.

'Yan kasar da dama sun bukaci gudanar da bincike domin hukunta wadanda ke da hannu cikin wannan badakala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI