DRC-EBOLA

An kawo karshen Ebola a Jamhuriyar Congo- WHO

Sama da mutane dubu 2 suka mutu a sanadiyar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Sama da mutane dubu 2 suka mutu a sanadiyar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, an yi nasarar kawo karshen cutar Ebola wadda ta barke a karo na 10 a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, yayin da ta jinjina wa gwamnatin kasar da sauran wadanda suka taimaka wajen yaki da cutar.

Talla

Duk da cewa, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi jinjina ga wadanda suka bada gundunmawar kawar da cutar Eboba a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, amma ta yi gargadin cewa, akwai bukatar ci gaba da sanya ido tare da agaza wa mutanen da suka kubuta daga annobar.

A cikin sanarwar da ta raba wa manema labarai ciki har da RFI Hausa, shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, a halin yanzu duniya na da kayayyakin yaki da cutar ta Ebola kuma tuni aka bada lasisin riga-kafinta, sannan kuma an gano hanyoyin magance ta.

Shugaban Hukumar ta WHO ya ce, ya kamata a yi bikin wannan lokaci na kawo karshen cutar, amma kuma kar a kuskura a shantake saboda a cewarsa, kwayoyin cuta basa sassauci.

Sanarwar ta kara da cewa, babban riga-kafin barkewar duk wata annoba, shi ne zuba jari a ingantaccen tsarin kiwon lafiya.

A ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2018 aka sanar da barkewar Ebola a Arewacin Kivu na Jamhuriyar Demokradiyar Congo, inda a jumulce aka samu asarar rayukan mutane dubu 2 da 287 daga cikin mutane dubu 3 da 470 da suka harbu da ita.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke fama da sabuwar cutar coronavirus, kuma darasin da aka dauka daga cutar Ebola na taimakawa wajen tunkarar Covid-19 a cewar sanarwar ta WHO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.