Najeriya

Rikici ya mamaye jam'iyyar APC

Bisa dukkan alamu ana cigaba da samun baraka a Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, sakamakon dakatar da shugaban ta Adams Oshiomhole da kuma samun halartaccen wanda zai jagoranci jam’iyyar.

Shugaba Buhari da tsohon Shugaban jam'iyyar APC Oshiomhole
Shugaba Buhari da tsohon Shugaban jam'iyyar APC Oshiomhole RFI Hausa
Talla

A jiya Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin halartar taron shugabannin gudanarwar Jam’iyyar da bangaren Victor Giadom ya kira, abinda ya batawa bangaren Bola Ahmed Tinubu rai, wadanda ke goyan bayan bangaren Prince Hilliard Eta dake cewa ba zasu halarci taron ba.

Rahotanni sun ce Giadom na samun goyon bayan Gwamna Nasir El Rufai da Kayode Fayemi da Simon Lalong da Abubakar Badaru da kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi, yayin da bangaren Tinubu ke da Gwamna Abdullahi Ganduje da wasu gwamnoni 17.

Garba Shehu dake Magana da yawun shugaba Buhari yace shugaban kasa ya goyi bayan Giadom ne saboda bin umurnin kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI