Najeriya

An samu karin mutane dake dauke da Covid 19 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya tace adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya kai 20,020, sakamakon samun mutane 649 da suka harbu a jiya laraba, kuma 542 sun mutu.

Wasu daga cikin ma'aikatan dake yaki da Coronavirus
Wasu daga cikin ma'aikatan dake yaki da Coronavirus RIJASOLO / AFP
Talla

Hukumar yaki da cututtukar kasar tace daga sabbin mutanen 649, 250 sun fito ne daga Lagos, 100 a Jihar Oyo, 40-40 a Jihohin Filato da Delta, 28 a Abia, 27 a Kaduna, 22 a Ogun, 20 a Edo, 18 a Akwa Ibom, 17-17 a Kwara da Abuja, kana 14 a Enugu.

Hukumar tace an samu mutane 13-13 a Niger da Adamawa, 7 a Bayelsa, 6-6 a Osun da Bauchi, Anambra na da 4, Gombe na da 3, Sokoto na da 2, Imo da Kano na da guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI