Shugaban Senegal ya killace kansa saboda coronavirus
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Senegal ta ce shugaban kasar Macky Sall ya kebe kansa na tsawon makwanni biyu sakamakon mu'amalar da ya yi da wani mai dauke da cutar coronavirus cikin rashin sani, amma gwajin farko ya nuna cewa, ba ya dauke da cutar.
A jawabinsa ta kafar talabijin, kakakin gwamnatin kasar Seydou Gueye, ya ce shugaba Sall ya kebe kansa kamar yadda masana kiwon lafiya suka ba shi shawara.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta fara sassauta dokar hana zirga-zirgar da ta kafa don hana yaduwar annobar coronavirus, yayin da adadin masu dauke da cutar ya kai dubu 6 da 100, inda 93 suka mutu a sanadiyarta.
Tun bayan bullar annobar shuagabannin siyasa da dama sun harbu da cutar a sassan duniya da suka hada da Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu