Habasha ta yi biris da Masar da Sudan kan Madatsar ruwa

Madatsar ruwa dake kogin Blue Nile a kasar Habasha
Madatsar ruwa dake kogin Blue Nile a kasar Habasha EDUARDO SOTERAS / AFP

Kasar Habasha ta nanata cewa, za ta ci gaba da aikin cike madatsar ruwan kogin Nile, da ake rikici akai na tswon shekaru da makwabtan ta Masar da Sudan dake Gabashin Afirka ko da kuwa ba’a kai ga cimma yarjejeniya.

Talla

Kasar Habasha tace, ko ana ha maza ha mata, babu abin da zai hana ta ci ga da kammala aikin gina madatsar ruwan wanda tuni ta gina kashi 70 na aikin da ta ware dalar Amurka biliyan 4 da miliyan 600 don samar wa al’ummarta kimanin miliyan 100 wutan lantarki.

Ministan harkokin wajen Habasha Gedu Andar-gachew ya bayyana hakan ga manema labarai jumma’a nan, inda yace, daga watan Yuni mai kamawa zasu ci gaba da aikin ko da kuwa ba’a kai ga cimma yarjejeniya da kasashen makobta da kogin ya ratsa Masar da Sudan.

Sama da shekaru goma ke nan kasashen Masar da Sudan ke jayeyya da Habasha kan shirinta na gina madatsan ruwan, matakin da zai kai ga kasashen biyu more ruwan da suke dogaro da shi, abin da yasa Masar din ta shigar da koke gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a makon da ya gabata.

Masar, wacce ke kusan dogara da Kogin Nile don samar wa al’ummata ruwan sha, na matukar bukatar samar da wata yarjejeniyar da zata bada tabbacin damar gudanar ruwa ko da bayan kammala madatsar da Habasha keyi.

Itama kasar Sudan a wata wasika da ya aikawa Kwamitin Tsaron na MDD ranar Alhamis, tayi gargadin cewar miliyoyin jama’a zasu fada cikin halin kakanikayi muddin kasar Habasha tayi gaban kan ta wajen cike madatsar ruwan ba tare da kulla yarjejeniya tsakanin ta da Masar da ita ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI