Wasanni

Liverpool ta lashe gasar Firimiya ta 2020

Yan wasan Liverpool,kungiyar da ta lashe gasar Firimiya
Yan wasan Liverpool,kungiyar da ta lashe gasar Firimiya Ibraheem Al Omari/Reuters

Kungiyar kwallon kafar Liverpool a Ingila tayi nasarar lashe gasar firimiyar bana, abinda ya kawo karshen shekaru 30 da tayi tana jiran lashe kofin.Nasarar ta biyo bayan doke Manchester City da Chelsea tayi daren jiya Alhamis da ci 2-1, sakamakon da ya nuna cewar yanzu City ba zata iya kama Liverpool dake da maki 86 a teburin firimiya ba, koda ta lashe sauran wasannin ta guda 7, ita kuma Liverpool ta barar da na ta.

Talla

Wannan shine kofin gasar Ingila da Liverpool ta lashe tun daga shekarar 1990, kuma shine kofin Firimiya na farko da kungiyar ta samu tun daga lokacin da aka sauyawa gasar suna a shekarar 1992, yayin da abokiyar gabar ta Manchester United ta lashe kofin har sau 13.

Mai horar da Yan wasan Liverpool, Jurgen Kloop ya fashe da kuka bayan da ta tabbata cewar sun zama zakara, nasarar da ta biyo bayan lashe kofin zakarun Turai da na kungiyoyin duniya da kungiyar ta samu.

Cikin hawaye Kloop yace wannan shine lokacin da yayi ta fatar gani, inda ya bukaci magoya bayan kungiyar da su zauna cikin gidajen su domin nuna farin cikin su saboda annobar COVID-19.

Wannan bai hana fitowar dubban magoya bayan kungiyar ba a birnin Liverpool sanye da kyallen rufe baki da hanci suna bayyana farin cikin su da gagarumar nasarar da suka dade suna jira.

Yanzu haka ana cigaba da mika sakon taya murna ga kungiyar, kuma cikin wadanda suka aike da sakon su hada da fitaccen yan wasan kwandon Duniya LeBron James da Samuel L Jackson da tsohuwar tauraruwar kwallon tennis Caroline Wozniacki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI