Nijar

Yan Bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikata a kauyen Tillabery

Wasu daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a yankin Tillabery daf da kan iyaka da Burkina Faso
Wasu daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a yankin Tillabery daf da kan iyaka da Burkina Faso MICHELE CATTANI / AFP

Yan bindiga dauke da mugan makamai sun yi awon gaba da ma’aikatan wata kungiya mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar mai suna Apis a kauyen Makalondi dake jihar Tillabery.

Talla

Ranar Laraba da ta gabata ne, wasu mayakan jihadi suka yi awon gaba da wasu ma’aikata na kungiya mai zaman kan ta mai suna Apis a dai-dai lokacin da suke rabon cimaka a wani kauye dake kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar daf da kan iyaka da Burkina Faso.

Shugabar wannan kungiya ta Apis Kadidaitou Harouna dake aiki kafada da kafada da hukumar Abinci ta Duniya ta sheida cewa masu da’awar jihadin sun shigo gari ne saman Babura,inda suka yi awon gaba da ma’aikatan ,tareda suace motoci guda biyu da kungiyar ke aiki da su.

Wannan dai ne karo na farko da aka taba fuskantar irin wannan matsala a cewar Kadidiatou Harouna ,wace ta sanar da cewa a shekara da ta gabata jami’an ta sun gudanar da irin wannan aiki a wasu wuraren inda aka haramta Babura da rana ko dadare kama daga farkon watan janairu da ya gabata.

Masu da’awar jihadi sun yi awon gaba da jami’an ne a wani kauyen Makalondi dake yankin Tillabery,yankin dake fuskantar matsallar tsaro.

A shekara ta 2018, wani dan kasar Jamus da wani limamu coci ne aka yi awon gaba da su ,kazalika yan bindigar na amfani da makamai da suke barazana da su don sauce motocin wadanan kungiyoyi..

A watan Disembaq na shekarar bana dai ne zaben Shugaban kasa da nay an Majalisu, a kasar ta Nijar,dake ci gaba da fuskantar hare-haren yan bindiga duk da karin sojojin Faransa 5.100 a rundunar barkhane dake fada da wadanan yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI