Benin

Yan fashin teku sun sace yan kasar Koriya a Benin

Yankin da yan Fashi saman teku ke cin karnen su
Yankin da yan Fashi saman teku ke cin karnen su US Navy/ Cmdr Michael Junge

Kungiyar Sufurin jiragen ruwa ta duniya tace Yan fashin teku sun sace wasu Yan kasar Koriya ta kudu guad 5 da dan kasar Ghana guda lokacin da suka kai hari kan jirgin ruwan su kusa da gabar ruwan Jamhuriyar Benin.

Talla

Rahotanni sun ce an kai hari kan jirgin ruwan su dake dauke da tutar Ghana ne a ranar larabar da ta gabata, inda aka sace mutane 6 daga cikin matuka jirgin 30.

Sanarwar tace ya zuwa yanzu babu wani bayani daga yan fashin.

Yan Fashi na amfani da wannan yanki domin sace ko kuma yin garkuwa da ma’aikatan jiragen ruwa.

Manyan kasashe da jimawa sun sha gargadin hukumomin kasashen yankin don ganin sun karfafa matakan tsaro a gabar tekun Guinea musaman jamhuriyar Benin,Togo,Ghana da Cote D’Ivoire baya ga yankin Somalia wurin da yan kungiyar Al Shebab suak yi kaurin suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.