Lafiya

Amurka ta fi yawan mutane da suka kamu da Coronavirus a Duniya

Wasu likitoci na gudanar da gwaji a kan wata mata
Wasu likitoci na gudanar da gwaji a kan wata mata CLEMENT MAHOUDEAU / AFP

Adadin Mutanen da cutar coronavirus ta kashe a Duniya ya kai 494,337, yayin da wadanda suka kamu da cutar suka kai miliyan 9 da dubu 823,840, kana miliyan 4 da dubu 882,900 sun warke.

Talla

Hukumar Lafiya tace har yanzu Amurka ta fi samun yawan mutanen da suka mutu, inda take da 125,039, daga cikin mutane kusan miliyan 2 da rabi da suka kamu da cutar a kasar, sai Brazil wanda ta samu mutuwar mutane 55,961, sai Birtaniya mai mutane 43,414, sannan Italia mai mutane 34,708, sai kuma Faransa mai mutane 29,778.

Alkaluman hukumar Lafiyar sun ce mutanen da suka mutu a Turai sun kai 195,655, sai Kudancin Amurka mai 108,222, Asia na da 32,439, Gabas ta Tsakiya na da 15,046 sannan Afirka mai mutane 9,250.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI