Gwamnatin Najeriya ta ki hukunta wasu Yan Sanda
Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da kin hukunta wasu daga cikin jami’an rundunar Yan Sanda dake yaki da Yan fashi da makami da aka zarga da aikata kisan gilla da kuma cin zarafin Bil Adama shekaru 3 bayan aikata laifin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotan da kungiyar ta gabatar tsakanin watan Janairu na shekarar 2017 zuwa watan Mayun da ya gabata, ya bayyana laifuffuka 82 na azabtarwa da cin zarafi da kuma kisan gilla da jami’an rundunar Yan Sandan suka aikata amma har ya zuwa yanzu babu wani jami’I da aka hukunta.
Rundunar Yan Sandan Najeriya bata mayar da martini dangane da wannan zargi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu