Afrika

Sudan,Masar da Habasha zasu kulla yarjejeniya dangane madatsar ruwan Nil

Kogin Nil a kasar Masar
Kogin Nil a kasar Masar RFI Hausa

Shugabannin Kasashen Sudan da Masar da kuma Habasha sun ce nan da yan makwanni masu zuwa zasu kulla yarjejeniya dangane madatsar ruwan da Habasha keyi, wanda Sudan da Masar ke korafi a kai.

Talla

Ministan ruwan Habasha Seleshi Bekele yace sun amince su kamala tattaunawa a tsakanin su nan da makwanni 2 zuwa 3 masu zuwa, kwana guda bayan wani taro da suka yi ta bidiyo wanda shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa dake jagorancin kungiyar kasashen Afirka ya shugaban ta.

Mai Magana da yawun Firaministan Habasha, Billene Seyoum tace a taron da suka gudanar jiya, babu wani abu da ya sauya dangane da shirin kasar na fara cike madatsar ruwan kasar, yayin da Masar tace Habasha ba za tayi gaban kan ta wajen cike madatsar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI