Malawi

Sabon shugaban Malawi ya yi alkawarin hada kan kasa

Zababben shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya sha alwashin hada kan al’ummar kasar bayan ya kada shugaba mai ci Peter Mutharika a zaben da suka fafata.

Zababben shugaban Malawi, Lazarus Chakwera
Zababben shugaban Malawi, Lazarus Chakwera AMOS GUMULIRA / AFP
Talla

Chakwera wanda tsohon mai bishara ne, ya samu kashi 59 na kuri’un da aka kada, abin da ya ba shi nasara akan shugaba mai ci.

Kafin bayyana sakamakon, Mutharika ya yi zargin tafka kura-kurai a zaben, inda ya bukaci a soke shi da kuma sake gudanar da wani.

Malawi ce kasa ta biyu a kudu da sahara da kotu ke soke zaben da aka yi, bayan samun haka a Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI