Masar-Habasha-Sudan

AU kan iya sasanta rikicin Masar Habasha da Sudan kan Madatsar ruwa- MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tattauna rikicin da ke kokarin barkewa tsakanin kasashen Masar da Sudan da kuma Habasha sakamakon shirin gina madatsar ruwan da Habasha ke yi.

Talla

Kwamitin ya yabawa kungiyar kasashen Afirka ta AU kan matakin da ta dauka na shiga cikin lamarin a daidai lokacin da kasashen ke tauna tsakuwa dangane da aikin.

Ashish Pradhan, jami’in Majalisar ya ce taron ya biyo bayan matsin lamba daga bangarori da dama amma kuma daukar matsayi na iya yin illa ga shirin kungiyar kasashen Afrika ta AU na sasanta rikicin.

Daraktan kungiyar ICG da ke Afirka Confort Ero ta ce kungiyar AU na da makwanni biyu wajen shawo kan kasashen su amince a tsakanin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI