Nijar

Ficewar Bazoum a gwamnati ya tilasta Nijar garambawul ga Majalisar ministocinta

Tsohon ministan cikin gidan Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum, da ke shirin fafatawa a zaben kasar mai zuwa don neman kujerar shugaban kasa.
Tsohon ministan cikin gidan Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum, da ke shirin fafatawa a zaben kasar mai zuwa don neman kujerar shugaban kasa. CCAS4.0 / Benhamayemohamed /Wikimedia Commons

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kwarya kwarya garambawul a Majalisar ministocin kasar wanda ya kunshi ficewar ministan cikin gida Bazoum Mohammed daga gwamnati domin fuskantar takarar zabe mai zuwa.

Talla

Sanarwar da gwamnati ta fitar ta bayyana cewa Alkache Alhada wanda ministan tsaron al’umma ne zai maye gurbin Bazoum a matsayin ministan cikin gida.

Bazoum na daya daga cikin jiga jigan gwamnatin PNDS Tarayya da shugaba Mahamadou Issofou ke jagoranci, kuma tun kafa gwamnati a shekarar 2011 ya rike mukamin ministan harkokin waje da na cikin gida.

Ana saran gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisu zagaye na farko ranar 27 ga watan Disambar wannan shekara, inda ake saran Bazoum ya fafata da gogaggun yan siyasa irin su Hamma Amadou da Seyni Oumarou da Mahamane Ousmane da Ibrahim Yakouba da kuma Janar Salifou Jibo mai ritaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI