Macron zai halarci taron kasashen Sahel a Mauritania
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na shirin halartar taron shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar G5 Sahel da zai gudana a Mauritania don tattauanwa kan batutuwan da suka shafi matsalolin tsaron da ya addabi yankin.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun hare-hare ta’addanci dana tsageru da kuma kungiyoyin da ke dauke da makamai masu ikirarin jihadi a yankin, duk kuwa da kasancewar tarin Sojin Faransa da ke taimakawa a yaki da ta'addancin.
Cikin shugabannin da za su halarci taron na yau Talata, har da shugaban kasar Burkina Faso dana Mali kana na Nijar da Chadi da kuma shugaban Mauritania da ke matsayin mai masaukin baki.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gudanar da makamancin taron ba, duk dai karkashin kokarin da ake na yaki hare-haren da yankin ke fuskanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu