Tattalin arzikin Afrika zai shiga tsaka mai wuya- IMF

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce annobar coronavirus na iya haifar da matukar koma baya dangane da cigaban tattalin arzikin da aka kwashe shekaru ana samu, saboda faduwar farashin mai da katsewar harkokin yawon bude ido da kuma harkokin kasuwanci.

Tambarin asusun bada lamuni na duniya IMF
Tambarin asusun bada lamuni na duniya IMF AFP/ Getty Images
Talla

Daraktan asusun na IMF mai kula da sashen Afirka Aemro Selassie ya ce halin da ake ciki yanzu abin fargaba ne dangane da hasashen tattalin arzikin nahiyar da kuma cigaba da tabarbarewar tattalin arzikin da ake gani.

Asusun ya ce ganin yadda farashin mai ya fadi a kasuwannin duniya, tattalin arzikin Najeriya zai fadi da kusan kashi 5 da rabi, sai kuma na Angola da shima zai fadi da kashi 4 a matsayinsu na kasashe nahiyar mafiya fitar da mai da kuma suka dogara da bangaren wajen samun kudaden shiga.

Asusun ya yi gargadin cewa illar da ke tunkaro tattalin arzikin na Afrika ya wuce yadda ake hasashe.

Hukumomin kudi na duniya daban-daban na ci gaba da gargadin koma bayan da coronavirus za ta haifarwa nahiyar mai fama da talauci hare-haren ta'addanci da kuma rikicin siyasa da rashin daidaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI