Kashen G5 Sahel zasu karfafa yaki da ta'addanci

Shugabanni Kasashen G5 Sahel da na Faransa sun amince da shirin karfafa yakin da suke da Yan ta’adda a Yankin Sahel bayan wani taro da yayi Nazari kan yadda yakin ke gudana da akayi a kasar Mauritania.

Taron shugaban kasashen G5 Sahel a Maurtania
Taron shugaban kasashen G5 Sahel a Maurtania Ludovic Marin /Pool via REUTERS
Talla

Yayin taron a Nouakchott na kasar Maurtania shugabannin kasashen dake kawancen yaki da ta’addanci a Sahel sun yi bitar nasarori da kuma kalubalen da suke fuskanta tun bayan sabunta salon yaki da masu ikirarin Jihadin da suka yi a watan Janairun da ya gabata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce babban makasudin taron na baya bayan nan shi ne tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu a baya da kuma gyara kura-kuran da aka samu, gami da daukar sabbin matakan da bai yi karin haske a kansu ba.

Sai dai daya daga cikin batutuwa da taron ya maida hankali shi ne tsaurara sa ido kan iyakokin da suka hada kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar inda hare-haren ta’addancin suka fi kamari.

Yayin jawabi a taron mai masaukin baki shugaban kasar Mauritania Muhd Ould Shiekh Ghazouani ya ce ba shakka sun samu nasarori da dama kan mayakan na ‘yan ta’adda to sai dai sun gaza shawo kan tarin kalubalen da har yanzu suke fuskanta, la’akari da yadda akidar ta’addancin ke dada bazuwa a sassan yankin Sahel cikin sauri.

Yanzu haka dai Faransa mai kimanin dakaru Dubu Biyar dake jagorantar rundunonin kasashen G5 Sahel wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin, ta kara azama wajen kawo karshen mayakan da Abu Walid al-saharawi ke jagoranta, wadanda suka yiwa IS mubaya’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI