Libya

Salame ya zargi kwamitin Sulhu da munafurtar kokarinsa na sasanta rikicin Libya

Tsohon Jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Libya Ghassan Salame ya zargi kwamitin sulhu da munafunci a kokarin da ake na sasanta rikicin, inda ya ce wakilan kwamitin sun masa zagon kasa lokacin da yake gudanar da aikinsa.

ប្រេសិតអ.ស.ប ប្រចាំប្រទេសលីប៊ី លោកហ្គាសាន់ សាឡាម (Ghassan Salame)
ប្រេសិតអ.ស.ប ប្រចាំប្រទេសលីប៊ី លោកហ្គាសាន់ សាឡាម (Ghassan Salame) REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Salame wanda ya bayyana sauka daga mukamin sa a watan Maris saboda dalilan rashin lafiya bayan ya kwashe shekaru 3 yana fafatawa, ya bayyana cewar wasu daga cikin wakilan kwamitin sulhun na goyan bayan yunkurin Janar Khalifa haftar na kwace birnin Tripoli.

Tsohon Jakadan ya ce harin da Haftar ya kai ranar 4 ga watan Afrilun bara ya haifar da tsaiko wajen shirin sasanta rikicin, yayin da wasu kasashe masu muhimmanci ke goya masa baya.

Salame ya ce a bayyana yake Janar Haftar na samun goyan bayan wadannan kasashe, abinda ya sa yake abinda ya ga dama ba tare da an taka masa birki ba.

Jakadan yace wannan ya nuna karara cewar munafurcin dake gindin wadannan kasashe ba zai bada damar samun nasarar sasanta rikicin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI