Isa ga babban shafi
Habasha

Rikicin da ya barke bayan kisan Mawaki a Habasha ya hallaka mutum 81

Wasu da suka tserewa rikicin kabilanci.
Wasu da suka tserewa rikicin kabilanci. www.kassfm.co.ke
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Akalla mutane 81 suka mutu sakamakon wata kazamar zanga zangar da ta biyo bayan kashe wani fitaccen matashin mawaki a kasar Habasha, Hachalu Hundessa, rikicin da ke neman durkusar da gwamnatin kasar, abinda ya sa ta baza sojoji domin tabbatar da tsaro.

Talla

Masu zanga zangar cikin fushi sun mamaye titunan biranen Addis Ababa da yankin Oromia, yankin da mutanen sa ke korafin cewar kananan kabilu sun mamaye a kasar dake dauke da mutane miliyan 100.

Babban jami’in 'yan sandan yankin, Ararsa Merdasa, ya sanar da mutuwar mutane 81 a rikicin, cikin su harda manyan jami’an su guda 3.

Jami’in ya ce yayin tashin hankalin an kai hari da gurneti gidan su mawakin da aka kasha Hachalu Hundessa, abinda yayi sanadiyar kasha kawun sa da kuma raunana wasu mutane 2.

Firaminista Abiy Ahmad ya danganta tashin hankalin da rikicin da kasar keyi da makotan ta wajen gina madatsar ruwa, yayin da jami’an tsaro suka kama wasu daga cikin shugabannin Yan adawar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.