Tawaga ta musamman za ta binciki shugaban bankin raya Afrika Adesina
Tsohuwar shugabar gwamnatin Ireland Mary Robinson za ta jagoranci binciken zargin da ake wa shugaban bankin raya Afrika Akinwumi Adesina kan badakalar rashawa da nuna fifiko da ta dabaibaye shugabancinsa.
Wallafawa ranar:
Matakin dai na zuwa bayan fitar wata wasika mai shafuka 15 da ke zargin shugaban bankin Akinwumi Adesina mai shekarun 60 da tarin laifuka, ciki har da rashin iya jagoranci, rashawa da kuma nuna banbancin wajen daukar ma’aikata.
Sai dai tun a wancan lokaci sauran shugabannin bankin da kwamitin da a na bankin sun musanta zargin yayinda suka nesanta fitar wasikar tuhumar daga tsakaninsu, sai dai shigar Amurka zancen a watan Mayun da ya gabata ya dawo da maganar sabuwa, wadda ke zuwa dai dai lokacin da Adesina ke neman wa’adi na biyu na shugabancin bankin.
Akinwumi Adesina dai shi ne dan Najeriya na farko da ya karbi jagorancin bankin a shekarar 2015.
Yanzu haka dai Mary Robinson tsohuwar lauya da ta jagorancin Ireland tsakanin shekarar 1990 zuwa 1997 ta kuma shugabancin hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya a 2002, ita ce za ta jagoranci binciken bisa rakiyar babban alkalin Gambia Hassan Jallow kana shugaban kwamitin ladabtarwa na bankin duniya Leonard McCarthy.
Tuni dai shugabancin bankin ya nuna kwarin gwiwa kan binciken.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu