Afrika

Mary Robinson zata jagoranci binciken Akinwumi Adesina

An nada tsohuwar shugaban kasar Ireland Mary Robinson don jagorantar ayarin masu binciken zargin da ake yiwa shugaban Bankin Raya Africa Akinwumi Adesina, dan Nigeria da ake zargi da karya dokokin aikin bankin.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina. AFP/Issouf Sanogo
Talla

Akinwumi Adesina ya kasance na farko daga kasar Najeriya da yake jagorancin wannan Banki tun shekara ta 2015.

Sai dai kuma a cikn wata takardar koke mai shafuka 15 a farkon wannan shekaran ke cewa a zamaninsa ayyukan bankin sun fuskanci matsalolli.

A binciken farko dai wani kwamytin da Bankin ya kafa ya wanke shi sumul daga dukkan zargin da ake masa.

Ita dai Uwargida Mary Robinson za tayi aikin binciken tare da Hassan Jallow Alkalin Alkalan kasar Gambia, sai kuma wani mataimakin shugaban Bankin Duniya Leonard MacCathy.

Ita dai Mary Robinson , Lauya ce, kuma ta shugabanci kasar Ireland tsakanin shekara ta 1990-1997 kafin ta koma Ofishin kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dimkin Duniya.

Ana sa ran samun rahoton binciken cikin makonni 2 zuwa 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI