Isa ga babban shafi
WHO

WHO ta shinfida wa Afrika sharuddan bude filayen jiragen sama

Filin jirgin sama na kasa da kasa na Murtala Mohammed da ke birnin Lagos na Najeriya.
Filin jirgin sama na kasa da kasa na Murtala Mohammed da ke birnin Lagos na Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye/File Photo
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
2 Minti

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci gwamnatocin kasashen Afrika da su dauki kwararen matakan kariya daga annobar coronavirus a daidai lokacin da suke shirin sake bude kan iyakokinsu don ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama.

Talla

Akasarin kasashen Afrika sun yi gaggawar daukar mataki wajen kulle jama’a a gidajensu da kuma takaita zirga-zirga don hana bazuwar cutar coronavirus jim kadan da bullarta a nahiyar, inda kasashe 36 suka rufe kan iyakokinsu na sama da na kasa, yayin da guda takwas suka dakatar da shigowar jiragen saman daga kasashen da wannan annoba ta fi ta’azzara.

Kawo yanzu kasashen Kamaru da Tanzania da Equitorial Guinea da Zambia sun fara jigilar fasinjojin jiragen sama, yayin da ake sa ran mambobin kasashen Kungiyar Yammacin Afrika 15 za su bude nasu iyakokin na sama nan da ranar 21 ga watan Yuli.

Darektan Hukumar Lafiya ta Duniya shiyar Afrika, Matshidiso Moeti ta ce, zirga-zirgar jiragen sama na da muhimmanci ga tattalin arzikin kasashe, amma fa, akwai bukatar tsaurara matakai don hana bazuwar COVID-19 a cewarta.

Hukumar Lafiyar ta Duniya ta shawarci kasashen da su tantance yanayin halin da ake ciki domin sanin ko ci gaba da takaita zirga-zirgar ya fi muhimmanci fiye da sake bude kan iyakokin, ma’ana dai, idan cutar ta ci gaba da mummunar bazuwa.

Kazalika Hukumar ta WHO ta ce, lallai yana da muhimmanci a tantance ko tsarin lafiyar kasashen na Afrika na da karfin tunkarar matsalar dauko cutar daga wata kasa ko kuma suna da ingantaccen tsarin bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar tare da sanya ido a kansu..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.