Faransa-Rwanda

Kotun Faransa ta kori bukatar sake bincike kan kisan tsohon shugaban Rwanda

Tsohon shugaban kasar Rwanda Juvénal Habyarimana.
Tsohon shugaban kasar Rwanda Juvénal Habyarimana. AFP

Babbar kotun daukaka kara a Faransa ta kori bukatar sake bude bincike kan kisan gillar da aka yiwa tsohon shugaban Rwanda Juvenal Habyarimana a shekarar 1994.

Talla

Wadanda suka nemi sake gudanar da binciken kisan gillar dai sun hada da iyalan makusantan Habyarimana da suka mutu tare bayan harbo jirginsu da aka yi da makami mai linzami a birnin Kigali, wadanda tuni suka sha alwashin daukaka kara zuwa kotun kolin Faransa.

Babban burin iyalan dai shi ne rushe hukuncin kotun daukaka karar Faransa dake Paris a 2018, da yayi watsi da binciken da aka bude kan wasu jami’an gwamnatin shugaban Rwanda Paul Kagame, batun da ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen 2 na Rwandar da Faransa.

Ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 1994, aka yi amfani da makami mai linzami wajen harbor jirgin saman dake dauke da tsohon shugaban Rwanda dan kabilar Hutu Juvenal Habyarimana, tare da tsohon shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira, abinda ya janyo rikicin da ya kai ga yiwa mutane dubu 800 kisan gilla, mafi akasarinsu ‘yan kabilar Tutsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.