Isa ga babban shafi
Coronavirus-Afrika

Kusan rabin wadanda suka kamu da coronavirus a Afrika sun warke - ACDC

Wasu ma'aikatan lafiya a daya daga cikin cibiyoyin gwajin cutar coronavirus a birnin Johannesburg dake Afrika Kudu. 15/4/2020.
Wasu ma'aikatan lafiya a daya daga cikin cibiyoyin gwajin cutar coronavirus a birnin Johannesburg dake Afrika Kudu. 15/4/2020. Michele Spatari/AFP/Getty Images
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Hukumar kula da dakile yaduwar cutuka ta Afrika ACDC, tace kusan rabin sama da mutane dubu 400 da suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar sun warke.

Talla

Kafin wannan lokacin dai hukumomi da dama ciki har da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi hasashen cewar yawan masu dauke da cutar a Afrika ka Iya zarta miliyan 10, wasu kusan 300 kuma su halaka, saboda rashin ingancin tsarin kula da lafiya.

Sai dai har yanzu kashi 5 kawai cikin 100 na yawan wadanda annobar ta coronavirus ta halaka a duniya Afrika ke da shi.

Zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Yulin 2020, hukumar dakile yaduwar cutuka a Afrika tace kimanin mutane dubu 195 da 729 suka warke daga coronavirus, daga cikin jumillar dubu 414 da suka kamu, yayinda dubu 10, 260.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.