Isa ga babban shafi
Mali

'Yan ta'adda sun kashe dakarun Mali 7

Wasu sojojin Mali yayin sintiri a birnin Gao. 26/2/2013
Wasu sojojin Mali yayin sintiri a birnin Gao. 26/2/2013 Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Gungun ‘yan bindiga sun halaka sojojin Mali 7 bayan kwanton Baunar da suka yi wa dakarun a yankin tsakiyar kasar, a wani kauye da suka halaka akalla fararen hula 32.

Talla

Kakakin ma’aikatar tsaron Mali Kanal Diarran Koneman, yace ‘yan bindigar sun kaiwa sojin na Mali farmakin ne a wajen kauyen Gouari dake yankin Mopti.

Tun a ranar larabar da ta gabata gungun ‘yan ta’adda suka afkawa kauyukan Gouari da Djindo da Fangadougou tare da halaka mutane 32, kwana guda bayan hakan ne kuma mayakan suka sake dawowa a ranar alhamis inda suka kaiwa dakarun sojin da aka girke sabon farmakin.

Wani jami’in gwamnati da ya nemi sakaya sunansa, yace bayaga kisan sojojin, mayakan sun kuma lalata motocin sulke akalla 4.

Sabon farmakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan taron da hadin gwiwar da aka yi tsakanin kasashen G5 Sahel da Faransa kan matsalar ta’addanci a yankin, taron da ya samu halartar shugaba Emmanuel Macron a kasar Mauritania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.