Sabon Firaministan Faransa ya bayyana manyan manufofinsa
Sabon Firaministan Faransa Jean Castex da kammala ziyara sa ta farko a wata masana’anta a jiya lahadi,ya gabatarwa manema labarai da wasu daga cikin manyan manufofinsa biyo bayan maye gurbin Edouard Philippe.
Wallafawa ranar:
Jean Castex sabon Firaministan Faransa da Shugaba Macron ya nada a ranar asabar,a wata tattaunawa da jaridar Journal du Dimanche na kasar ta Faransa ya bayyana cewa ya na da yekinin ganin an magance matsallar yan fansho na kasar.
Jean Castex ya na mai cewa a shirye yake ya shiga tattaunawa da kungiyoyin kwadago tareda shifuda wata siyasa da zata sake dawo da jituwa da yarda tsakanin gwamnati da kungiyoyi dake kare hakkokin ma’aikata a Faransa.
Ga duk alamu bayyanan sabon firaministan faransa na sake komawa tattaunawa da kungiyoyin kwadago, hakan bai kawo wani sauyi ga siyasar farko da Shugaban kasar Emmanuel Macron ya shifuda ba, a maimakon samun wani gaggarumin sauyi, Jean Castex da ya maye gurbin Edouard Phillipe ya na mai jaddada ci gaba da manufofin Shugaba Macron.
Jean Castex ya karasa da cewa batun kare muhalli ya zama wajibi ba wai zabi ba.
A karshe Jean Castex ya na mai fatan sake shiga tattaunawa da bangaren jami’an kiwon lafiya daga mako na sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu