Isa ga babban shafi
Ghana

Shugaban Ghana ya killace kansa duk da gwaji ya nuna bashi da corona

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. Paul Marotta/Getty Images
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya killace kansa tsawon makwanni 2 saboda coronavirus, duk da cewa gwaji ya nuna baya dauke da cutar.

Talla

Ministan yada labaran Ghana Kojo Oppong Nkrumah, ya ce shugaban ya dauki matakin ne domin rigakafi, bayan da gwaji ya nuna wani makusancinsa ya kamu da cutar ta corona.

Kawo yanzu Ghana na da jumillar mutane dubu 19 da 300 da suka kamu da wannan cuta, daga cikinsu kuma 117 suka mutu.

A karshen mako ne dai mataimakin ministan kula da kasuwanci a kasar ta Ghana Hon. Carlos Kingsley Ahenkorah yayi murabus, saboda karya ka'idar killace kansa da yayi, wanda daga bisani gwaji ya nuna ya kamu da cutar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.