Isa ga babban shafi
Kamaru

An soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnati da 'yan awaren Kamaru

Wani bangaren garin Kembong, dake kudu maso yammacin Kamaru, da rikicin 'yan aware ya lalata.
Wani bangaren garin Kembong, dake kudu maso yammacin Kamaru, da rikicin 'yan aware ya lalata. REUTERS/Josiane Chemou
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

'Yan aware a Kamaru sun sanar da soma tattaunawar sulhu da gwamnati a makon da ya kare, wanda karo na farko tun bayanda ‘yan awaren masu amfani da turancin ingilishi suka dauki makamai a shekarar 2017.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na reuters ya ruwaito daya daga cikin manyan jagororin ‘yan awaren Julius Ayuk Tabe da ake daurin rai da rai na cewar tattaunawar ta soma ne daga ranar Alhamis din da ta gabata, domin kawo karshen rikicin.

A 2017, rikici ya barke a yankunan masu amfani da turancin Ingilishi, bayan da jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen murkushe zanga zangar al’ummar yankin dake korafi kan maida su saniyar ware da gwamnati tayi sabanin takwarorinsu masu magana da Faransanci.

Zuwa yanzu dai rikicin yayi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 3, gami da tilastawa wasu dubban tserewa daga gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.