Coronavirus

'Yan Afrika ta Kudu sama da dubu 10 sun kamu da cutar corona cikin sa'o'i 24

Ma’aikatar lafiyar Afrika ta Kudu, ta sanar da gano karin mutane dubu 10 da 853 da suka kamu da cutar coronavirus jiya asabar, adadi mafi yawa da kasar ta gani cikin sa’o’i 24.

Wasu fasinjojin jirgin kasa a Afrika ta Kudu a birnin Pretoria cikin baiwa juna tazara domin kare yaduwar annobar coronavirus. 1/7/2020.
Wasu fasinjojin jirgin kasa a Afrika ta Kudu a birnin Pretoria cikin baiwa juna tazara domin kare yaduwar annobar coronavirus. 1/7/2020. AFP
Talla

Yanzu haka dai yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai dubu 187, da 977, daga cikinsu kuma dubu 3 da 26 sun mutu, bayan mutuwar karin mutane 74 a jiya asabar din.

Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewar, Afrika ta Kudu ke kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI