Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Condo

'Yan bindiga sun kashe sojoji a DRCongo

Daya daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a DRCongo
Daya daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a DRCongo Racove, Radio communautaire de la Vérité
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Akalla mutane 11 da suka hada da yan Sanda da sojoji ne suka rasa rayyukan su a wani harin kwantar bauna da wasu yan bindiga suka kai musu a arewa maso gabacin kasar Congo ranar asabar da ta gabata.

Talla

Rahotanni daga yankin na nuni cewa ana zargin mayaka daga wata kabilar matsafa a karkashin kungiyar Codeco.

Ranar juma’a da ta gabata dakarun kasar Congo sun sanar da samun nasarar kashe wasu mayaka na kungiyar Codeco 7 da sunan suna yaki don kare muradun wannan kabila.

Ranar 4 ga wannan watan da nuke cikin sa Fati Bensouda dake bincike da kuma shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta bayyana cewa kisan jama’a da ake ci gaba da yi a wannan yanki ya dada jan hankulan wannan kotu ,mai yiyuwa a kaddamar da bincike a kai don hukunta masu hannu a wannan kazamin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.