Isa ga babban shafi
Mali

Boubacar Keita ya gana da jagororin masu zanga-zangar Mali karon farko

Dandazo masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita a birnin Bamako na Mali.
Dandazo masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita a birnin Bamako na Mali. MICHELE CATTANI / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Jagororin masu zanga-zanga a Mali sun ci gaba da matsa lamba ga shugaba Ibrahim Boubacar Keita, matakin da ya tilasta mishi kiransu don tattaunawa irinta ta farko tun bayan fara boren nasu sakamakon tsanantar ayyukan ta’addanci rashin aikin yi da kuma takaddamar da ta dabaibaye zaben yankunan da ya gabata batun da ya fi tunzura masu zanga-zangar.

Talla

Da alamu ganawar ba ta samar da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu ba, la’akari da yadda jim kadan bayan fitowar jagororin zanga-zangar suka sabunta kiran ganin lallai shugaban ya yi murabus daga mulki.

Bukatar jagororin masu zanga-zangar ta neman murabus din shugaban na zuwa bayan tun a farko sun yi makamancin kiran da ya kai haduwar gamayyar shugabannin kungiyoyi ciki har da na addinai wajen gudanar da zanga-zangar irinta ta farko mafi karfi da Mali ta taba gani a tarihi don neman murabus din shugaban.

Hoton bidiyo da fadar gwamnatin Mali da wallafa a shafinta na Twitta ya nuna ganawar ta shugaba Keita da gamayayyar kungiyoyin karkashin jagorancin fitaccen malamin addini na kasar Mahmoud Dicko.

Sanarwar da jagororin masu zanga-zangar suka fitar bayan ganawar ta jiya Lahadi, sun ce shugaban kasar ta Mali ya yi watsi da bukatun da suka mika masa ciki kuwa har da bukatar rushe majalisar dokoki da kafa gwamnatin kawance wanda zai ba su damar fitar da Firaminista daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.